Tuna baya: Lokacin da aka yi Shugabanni 5 cikin 'Dan kankanin lokaci a Kasar Argentina

Publish date: 2024-08-24

Ga wadanda ba su da labarin cewa an taba samun Shugabanni 5 a kwanakin kadan a Kasar Argentina. Don haka ne wannan karo mu ka shiga littafin tarihi domin kawo maku yadda aka yi.

A 2001, Kasar Argentinaa da ke Nahiyar Amurka ta samu kan ta cikin wani hali na rikicin siyasa inda aka samu Shugabanni 5 cikin sama da mako guda. Hakan ya fara ne bayan da Shugaban Fernando de la Rua ya karya kudin kasar.

1.Fernando de la Rua

De La Rua ya sauka mulki ne a Ranar 20 na Disamban 2001 bayan ya karya darajar kudin kasar. De La Rua ya kuma haramtawa Jama'a cire kudi daga bankunan kasar.

KU KARANTA: Ba zan bar Buhari in kama Atiku ba - Tinubu

2.Ramon Puerta

Kafin nan dama Mataimakin Shugaban kasar yayi murabus. Don haka aka nada Shugaban Majalisa Dattawa Ramon Puerta a matsayin sabon Shugaban kasa.

3.Adolf Rodriguez Saa

Bayan Puerta ya bar kujerar ne a Rana ta karshe a karshen Disemba aka nada Adolf Saa wanda ya gaje Ramon Puerta.

4.Eduardo Camano

A Ranar 31 ga Watan Disamban ne kuma Adolf Saa yayi murabus shi ma. Na take. Eduardo Camano wanda shi ne babba a Gwamnatin ya dare mulkin.

5.Eduardo Duhalde

Shugaba Duhalde ya gaji Takwarar sa a farkon Watan Junairu bayan Eduardo Camano ya bar mulkin Kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kG1rcGllYsG2usBmmZqxkWK5sLfAnKCnZZSWeqK3wGawomWjncKorcGapaehXWp6pLXKoqVmnJGjeqytzaSYp6GeYrmwt8CcoGaZXaCutK3RZphnoKSiuQ%3D%3D