Tinubu Ya Dauki Wani Muhimmin Alkawari Bayan Hukuncin Kotun Koli Kan Kananan Hukumomi
- Shugaba Bola Tinubu ya yaba da hukuncin da kotun koli ta yanke na bayar da cikakken ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi
- Tinubu ya ce gwamnatinsa ta yi imanin cewa ba kananan hukumomi 'yanci ne hanya mafi dacewa ta kai ayyukan gwamnati ga jama’a
- Shugaban ya kara da cewa a yanzu kudin kananan hukumomi zai koma karkashin ciyamomi, inda ya ce jama’a za su rika sa ido kan hakan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya yi maraba da hukuncin kotun koli na ba kananan hukumomi ‘yanci, inda ya ce wannan nasara ce da ta shiga tarihin kasar nan.
Tinubu ya fadi sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata, NLC ta dage kan N250,000
Tinubu ya yi imanin cewa rashin ingantaccen tsarin gudanar da kananan hukumomi ne ya kawo cikas ga ci gaban Najeriya, kuma yanzu ya rage ga ciyamomi su yi ayyukan cigaba ga jama'arsu.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Cif Ajuri Ngelale ya fitar, jim kadan bayan yanke hukuncin a ranar Alhamis, wadda Dayo Olusegun ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya bayyana dalilin zuwa kotu
A cewar sanarwar, shugaban ya shigar da karar tun farko ne domin tabbatar da cewa zababbun shugabannin kananan hukumomi ne kawai suke da ikon dukiyar al’umma domin kawo sauki.
Ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta bayyana abin da aka aika a asusun kananan hukumomi, kuma jama’a za su yi wa ciyamominsu alkalanci kan gudanar da ayyuka.
Tinubu ya yi nuni da cewa barnatar da kudin kananan hukumomi da ake yi ya kawo cikas wajen samar da ababen more rayuwa da suka hada da gine-ginen tituna, tsaro, dasaukin rayuwa.
Kananan hukumomi: Shehu Sani ya faɗi yadda ciyamomi za su yiwa gwamnoni
Tinubu ya jinjinawa Antoni Janar na tarayya
Shugaban kasar yabawa babban mai shari’a na tarayya bisa kokarinsa tare da jaddada kudirinsa na kare ka’idojin kundin tsarin mulkin da ke kare ‘yan kasa da gwamnati.
Tinubu ya yi imanin cewa, wannan matakin zai inganta tsarin tarayyar Najeriya, wanda zai haifar da nagartaccen tsarin mulki da zai amfani dukkanin 'yan kasar.
Karanta cikakken bayanin anan kasa:
SERAP za ta yi karar gwamnoni 36
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar da ke rajin bin diddigin ayyukan tattali ta SERAP, ta aika sako ga gwamnonin jihohi 36 bayan hukuncin kotun koli.
SERAP ta sanar da bukaci gwamnonin kasar nan da ministan Abuja da su hanzarta ba da ba'asi kan kudin kananan hukumomi da suka karba tun daga 1999 zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZX55fpdmmZqxkaN6qcHKrqWcoZ5iuLDA1GaimqZdoK6vrc2apWagpaDCrrvMomStoZ6qr7Z52JpknZmloLZuw8CnoGalpZ22rrnIp2SapJuWxKK%2ByGg%3D