'Yan Sanda Sun Bue Wuta Yayin da Masu Zanga Zanga Suka Toshe Babban Titi a Arewa
- Jami'an ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a lokacin da suka yi yunkurin toshe babban titi a Minna, babban birnin jihar Neja
- An dai jiyo karar harbe-harben bindiga da matasan suka matsa sai sun toshe titin bayan sun fara zanga-zanga yau Alhamis
- Tuni dai aka ƙara girke jami'an tsaro a wurare masu muhimmanci waɗanda ake tunanin za a iya samun matsala a Minna
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Ƴan sanda sun yi ta harbe-harbe a saman iska a babbar mahadar titin Top Medical da ke unguwar Tunga a Minna, babban birnin jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a lokacin da masu zanga-zanga suka yi yunƙurin toshe babban titin yau Alhamis, 1 ga watan Augusta, 2024.
Kano: ’Yan sanda sun tashi tsaye, matasa sun farmaki shaguna daga fara zanga zanga
Me ya kawo harbe-harbe a Neja?
Tun da farko dai ‘yan sandan sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar amma suka sake haɗuwa da nufin ɗora duwatsu a titin mai tara cunkoso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ganin haka ne ya sa ƴan sanda sakin wuta a saman iska domin tsorata masu zanga-zangar su bar wurin.
Tuni dai ‘yan sanda da ‘yan banga suka kwashe duwatsun da masu zanga-zangar suka yi amfani da su wajen tare wani bangare na titin.
An girke 'yan sanda da jami'an tsaro
Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, sojoji, jami'an shige da fice, jami’an tsaron fararen hula NSCDC sun mamaye wuraren da ake tunanin zanga zanga za ta yi zafi a Neja.
Daga cikin wuraren da aka girke jami'an tsaron har da babban shataletalen Kpakungu wanda ke kan titin Minna zuwa Bida.
Ana fargabar miyagu za su shiga zanga zanga, an samu hanyoyi 5 domin kare kai
Rahoton The Nation ya nuna cewa an rufe shaguna da kasuwanni a Minna domin gujewa abin da ka iya zuwa ya dawo na sace-sace a lokacin zanga-zanga.
Zanga-zanga: An fara yunƙurin fasa shaguna
Ku na da labarin an fara samun matsala a Kano yayin zanga-zanga bayan wasu matasa sun yi yunkurin fasa shaguna a birnin.
An tabbatar da cewa matasan sun kai farmakin ne a 'Zoo Road' da ke birnin Kano inda suka fasa wasu tagogi yayin zanga-zangar da aka fara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZYJ2gpJmopqqkad6qa3Rm5xmoJGnr6Z52JqwoqZdma5uxcCnZKyZnpmubr%2FUpJhmoJGjrm7FwKdks5menK5uxsCnnpplpJ7AqbGMraCtoV2Weq%2B1xp6paA%3D%3D