Kananan Hukumomi: Tinubu, Gwamnoni Sun Yi Matsaya, ba Za a Aikawa Ciyamomi Kudinsu ba
- Da alamu 'yancin kananan hukumomin Najeriya zai iya samun tasgaro bayan fiye da wata daya kenan da hukuncin Kotun Koli
- Akwai alamun Gwamnatin Tarayya da Bola Tinubu za su iya fitar da matsaya kan tsawaita lokacin fara biyan kananan hukumomin
- Idan hakan ta tabbata, kananan hukumomin ba za su fara samun kudinsu daga Gwamnatin Tarayya ba sai nan da watanni uku
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ana kyautata zaton Gwamnatin Tarayya da gwamnonin jihohi za su tsayar da matsaka kan 'yancin kananan hukumomi.
Matsayar za ta kai har na tsawon watanni uku kafin tabbatar da 'yancin na su duba da yanayinsu da kuma biyan albashi.
Tinubu ya kuma gamuwa da cikas bayan kwace jiragen fadar shugaban kasa 3 a ketare
Yancin kananan hukumomi ya samu tasgaro
Punch ta tattaro cewa fiye da wata daya kenan da hukuncin Kotun Koli amma dokar ba ta fara aiki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Yulin 2024, yawan kudin da Gwamnatin Tarayya ke rabawa ya karu da N1.35trn yayin kananan hukumomi ke dauke da N337.01bn.
Matsayar na nufin kananan hukumomin za su jira har zuwa watan Oktoban 2024 kafin samun cikakken 'yancin, cewar New Telegraph.
Gwamnati ta yi magana kan biyan kudin
Gwamnatin Tarayya a ranar 25 ga watan Yulin 2024 ta tabbatar da cewa ba ta fara biyan kananan hukumomin 774 ba da ake yi kowane wata.
Ministan kudi, Wale Edun ya alakanta hakan da ka'idoji kan hukuncin Kotun Koli wanda ba ta sanar da Ministan Shari'a a kan lokaci ba.
Edun ya ce har yanzu ana kan matakin farko ne game da kananan hukumomin inda ya ce ana daukar wasu matakai da za su taho da karin bayani.
Bayan tabbatar da mafi ƙarancin albashi, an lissafa karin da ma'aikata za su samu
Wani ma'aikacin karamar hukuma a Gombe ya shaidawa Legit Hausa ra'ayinsa kan yancin kananan hukumomi.
Abubakar Isa ya ce daman ya sani gwamnoni za su yi duk mai yiwuwa wurin dakile lamarin.
"Tun bayan hukuncin kotu na ke kokwanton samun yancin, ga shi an fara samu tasgaro.""Muna rokon gwamnoni su yi hakuri su bari kananan hukumomi su samu yanci saboda ba tabbata za su yi kan mulki ba."- Abubakar Isa
Kotu ta dakile gwamnoni kan kananan hukumomi
A wani labarin, kun ji cewa Kotun Koli ta ba da sabon umarni game da hukuncin da ta yanke kan kananan hukumomi a Najeriya.
Kotun ta ba da umarnin cewa dole kowane kansila ko ciyaman ya shafe shekaru hudu a kan mulki kamar gwamnoni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZYR6hZZmq6KmpZfCbrDAZp6wmZ2jvK%2B1jKysp2WWnsGivoydmGalkanAosXAZqKapl2urq%2BvyKdknZldl7a6rc1mopqmkaOur3nHrqKupZ%2BitnA%3D